uventus na shirin sake daukar dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27, a bazara idan Old Trafford ta rage farashin da ta sanya a kan dan wasan na Faransa, wanda kwangilarsa za ta kare a bazarar 2022.
Kocin West Ham David Moyes ya ce Chelsea da Manchester United ba su tuntubi kungiyar ba a game da yiwuwar daukar dan wasan tsakiya Declan Rice, mai shekara 22, bayan da aka yi ta rade-radin cewa suna zawarcin dan wasan na Ingila.
Kazalika Moyes ya ce West Ham ta nemi biyan ‘yan wasanta “makudan kudi” amma ba su amince su karba ba.
Kwangilar dan wasan tsakiyar Netherlands Georginio Wijnaldum a Liverpool za ta kare a bazara kuma dan wasan mai shekara 30 ba zai sabunta zamansa ba domin yana son ya cika burinsa na tafiya Barcelona.
Post comments (0)