
Zan isar da saƙon ƴan Najeriya ga Buhari a kan kisan da Boko Haram su ka yi
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Intanet a Najeriya, Isa Ali Pantami, ya ce zai isar da saƙon al’umma ga Shugaba Muhammadu Buhari game da kisan mutum 43 da ‘yan […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Inter Milan na son karbo aron dan wasan Chelsea dan kasar Faransa Olivier Giroud, mai shekara 34, na tsawon wata shida, da kuma zabin sayensa. (Tuttosport via Mail)
Sai dai Inter za ta iya fuskantar kalubale daga wurin Juventus, a yayin da kocinta Andrea Pirlo yake son dauko ‘yan wasa hudu a watan Janairu, ciki har da Giroud. (Ilbianconero via Calciomercato- in Italian)
Chelsea za ta soma tattaunawa da dan wasan Bayern Munich David Alaba, mai shekara 28, a watan Janairu a yayin da take son daukar dan kasar ta Austria idan kwangilarsa ta kare a bazara mai zuwa. (AS via Sun)
Manchester United na fatan Villarreal za ta iya sake daukar tsohon dan wasanta, dan kasar Ivory Coast mai shekara 26 Eric Bailly, a wani bangare na neman kudin da suka kai £60m don sayen dan wasan Sifaniya Pau Torres, mai shekara 23. (Team Talk)
Barcelona ta ki amincewa da tayin euro 250m daga Inter Milan don sayen dan wasan Agentina Lionel Messi, mai shekara 33, a shekarar 2006, a cewar tsohon shugaban kungiyar Joan Laporta. (Football Italia)
Liverpool za ta iya daukar dan wasan Ajax Perr Schuurs idan ta mika £27m a kan dan wasan mai shekara 21. (De Telegraaf via Liverpool Echo)
Tottenham na sanya ido kan dan wasan Sassuolo Gian Marco Ferrari, mai shekara 28, a yayin da take son dauo dan wasan na Italiya a watan Janairu. (90min)
Manchester United na iya zawarcin dan wasan Inter Milan Christian Eriksen, mai shekara 28, idan Tottenham ba ta son daukar dan kasar ta Denmark. (Football Insider)
Golan Faransa da Fulham Alphonse Areola, mai shekara 27, ya ce ya yi watsi da tayin da kungiyoyi da dama suka yi na daukarsa ciki har da Real Madrid da Paris St-Germain domin ya zauna a kungiyarsa. (Canal+ via Football London)
Dan wasan Bayern Munich Javi Martinez, mai shekara 32, ya nuna alamar cewa zai bar kungiyar idan kwangilarsa ta kare a watan Yuni mai zuwa, yana mai cewa yana son “gwada wani sabon abu”. (Reuters via Eurosport)
Dan wasan AZ Alkmaar Mohamed Taabouni, mai shekara 18, na shirin tafiya Italiya ko Sifaniya a watan Janairu, yayin da kungiyoyi da dama ke son daukar matashin dan wasan na Netherlands. (Voetbal International – in Dutch)
Newcastle na son re daukar dan wasan Eintracht Frankfurt Jetro Willems, mai shekara 26, a matakin dindindin bayan an tilasta wa dan wasan na Netherlands ya katse zaman aron da yake yi a St James’ Park a watana Janairu saboda raunin da ya ji a gwiwarsa. (Shields Gazette)
BBC HAUSA
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Intanet a Najeriya, Isa Ali Pantami, ya ce zai isar da saƙon al’umma ga Shugaba Muhammadu Buhari game da kisan mutum 43 da ‘yan […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)