
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani February 11, 2021 8
Wani mai gidan haya mai suna Mufutau Ojomu a ranar Laraba ya bayyana a gaban wata kotun majistare da ke Ogudu a jihar Legas a kan zarginsa da ake da yi wa ‘yar haya mugun duka bayan ya bata notis.
‘Yan sandan suna zargin Ojomu da laifin hada kai wurin aikata laifi da cin zarafi, Vanguard ta wallafa.
Dan sanda mai gabatar da kara, Dojour Perezi, ya sanar da kotu cewa mai kare kan shi ya aikata laifin a ranar 27 ga watan Disamban 2020 a layin Yisa Omotunde da ke yankin Alapere a jihar Legas.
Ya ce wanda ke kare kansa da wasu da har yanzu basu shiga hannu ba sun kama Ruth David sun yi mata duka saboda notis da ya bata.
Ya ce wanda ke kare kanshi ya aikata laifin da zai iya kawo karantsaye ga zaman lafiya ta hanyar hayar ‘yan daba da suka zane wacce ke kara.
Ya ce wacce ke korafin bata rike da ko sisin mai gidan hayan. Wannan laifin ya ci karo da tanadin sashi na 173 da 411 na laifukan jihar Legas na 2015.
Duk da musanta laifinsa da yayi, alkali O.M Ajayi ta bada belinsa a kan N50,000 tare da dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Maris
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)