
Ƙungiyar jami’an kiwon lafiya da ke binciken cutuka ta ƙasa wato ARIN, ta ce rakuni na biyu na kullen COVID-19 ya kusanto saboda ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar korona a cikin makonnin da su ka gabata.
Shugaban reshen ƙungiyar na birnin tarayya Abuja Dokta Ohikhoakhai Wellington, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja.
Ohikhoakhai Wellington, ya ce tuni masana da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum su ka bayyana shekarar 2020 a matsayin shekarar annoba sakamakon cutar corona da illolin da take haifarwa a tsakanin al’ummomi da tattalin arziki.
Wannan dai yana zuwa a daidai lokacin da hukumar dakile ya duwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar da sanarwar samun karin mutum 180 a suka harbu da cutar Coronavirus a faɗin ƙasar nan.
A sakon da hukumar ta fitar a daran jiya ya nuna cewa adadin mutum 64,516 ne a ka tabbatar da sun kamu da cutar ta korona.
Post comments (0)