play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Lokaci ya yi da yan Najeriya za su dage da addu’a inji Sarkin Musulmi

Addini

Lokaci ya yi da yan Najeriya za su dage da addu’a inji Sarkin Musulmi

Bello Sani December 4, 2020


Background
share close

Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar musulmi da su yawaita zama masallatai suna addu’a domin samun waraka daga matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya yi wannan kira ne a wurin babban taron manoma da sarrafa Dibino a Najeriya da aka yi a Sokoto. Ya ce yin hakan zai iya yin tasiri sosai wajen samun mafita daga matsalolin rashin tsaro da ke haddabar kasar nan.

“Ina kira ga dukkannin mu musamman musulmi na wannan kasa, da mu rika tsayawa a masallatai idan muka je sallah sau biyar a rana, da kuma sallar Juma’a koma a duk inda muka samu kanmu, a ci gaba da yin addu’a ga wannan kasa domin neman gafara daga Allah da jin kai mu samu fita daga wannan kangi na kaluballale da muke fuskanta”.

Dangane kisan manoman Shinkafa da aka yi a jihar Borno, Mai alfarma sarkin musulmi ya nuna bacin rai.

Ya ce “Babban abin muni ne abin da ya faru a Borno ‘yan kwanakin da suka wuce, yana daya daga cikin kisa mafi muni da aka yi a kasar nan, amma dole mu koma ga Allah a koda yaushe domin shine ke yin yadda ya so a lokacin da yaso, ba muna kalubalantar hukuncin Ubangiji ba ne, sai dai muna kara gode masa akan, farkar da mu shugabannin ga hakkin da ya rataya akan mu domin zai tambaye mu akan nauyin da ya dora mana”.

Yin amfani da shawarwarin shugabannin addinai da na al’umma kan iya zama sila ta samarwa da mabiya ga abin da suke nema, musamman yanzu da jama’a ke ta kokawa a kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *