Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sallami dukkan mashawartansa na musamman (SA) banda mutum daya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito. Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da sakataren gwamnatin jihar na riƙo kuma shugaban ma’aikata, Alhaji Kabiru Balarabe, ya fitar.

Balarabe yace mai baiwa gwamna shawara ta musamman kan tsaro, Mai ritaya DIG Mamman Tsafe, shine kaɗai wanda zai cigaba da riƙe muƙaminsa. Wani ɓangaren jawabin yace: “Muna sanar da al’ummar Zamfara cewa, Gwamna Bello Matawalle, ya sallami dukkan masu ba shi shawara ta musamman daga muƙamansu, amma banda mai bada shawara kan tsaro.”

Balarabe ya umarci dukkan waɗanda abun ya shafa da su miƙa al’amuran ofisoshinsu zuwa ga daraktocin dake ƙarƙashin su. Hakanan kuma, Balarabe ya miƙa saƙon godiyar gwamna ga waɗanda wannan mataki ya shafa bisa gudummuwar da suka bada wajen cigaban jihar Zamfara

Leave a Comment

%d bloggers like this: