
Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma’aurata
Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil’adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani February 16, 2021 6
Yan Najeriya sun kwararawa wata budurwa sakonnin taya murna ga kyakkyawar budurwa yar Arewa bisa nasaran da ta samu.
Budurwar mai suna Maryam Musa ta yi sanarwa a shafin Tuwita bisa kammala karatun digirinta a fannin karatun lauya.
Maryam, wacce bata bayyana jami’ar da ta kammala ba ta godewa Allah bisa nasarar da ta samu.
Yan Najeriya sun jinjina mata bisa irin kyawun da Allah ya bata yayinda wasu ke taya ta murnan kammala karatunta.
Hakazalika wasu sun bata shawari kan rayuwa bayan karatu.
Wasu daga cikin mabiyanta a twitter sun bayyana ra,ayinsu kamar haka:
@AliyuIbrahimA13 yace: “Ina tayaki murna Barista. ina bukatar kyakkyawar lauya irinki, wacce za ta iya rikita Alkali.”
@Mushin24789 yace; “Ki kasance mai gaskiya duk inda kika samu kanki kuma kada kiyi rashin adalci a aiki…”
@Omacares1 yace: “Allah ya cigaba da kare ki da shiryar dake hanya madaidaici bisa wannan babban nasara.”
Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil’adama. Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)