play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right KO KUSAN AMSAR TAMBAYAR BARIN TAKUNKUMI A FUSKA YANADA ILLA KO HALAKA MUTUM?

Labarai

KO KUSAN AMSAR TAMBAYAR BARIN TAKUNKUMI A FUSKA YANADA ILLA KO HALAKA MUTUM?

Bello Sani February 8, 2021 4


Background
share close

A shafukan sada zumunta, ana ci gaba da yaɗa wani saƙo da ke bayyana cewa akwai hatsari a sanya takunkumin fuska mai ba da kariya daga ɗaukar cutar korona.

Sakon, wanda aka fi yaɗawa a Whatsapp kuma wanda bai ɗauke da sunan wanda ya ƙirƙire shi, ya lissafo haɗurran da mutum ka iya shiga ida ya sa takunkumin tsawon wani lokaci.

Asali ma, an bayyana cewa ana iya mutuwa idan aka bar shi a fuska sannan an bayar da shawarwari dangane da yadda ya kamata a sa takunkumin duk dai a cikin saƙon

Dangane da haka ne BBC ta tuntuɓi Farfesa Abubakar Sadiq Isa na Cibiyar Bincike a kan Cutuka masu Yaɗuwa ta Jami’ar Bayero da ke Kano.
Ya yi bayani kan wannan saƙo kuma ya amsa waɗannan tambayoyin:

Ko barin takunkumi a fuska tsawon wani lokaci na iya yi wa mutum illa?

Farfesa Abubakar Sadiq Isa ya ce wannan ba gaskiya ba ne. Ya ce a kimiyyance babu wata shaida da ke nuna cewa barin takunkumi a fuska tsawon wani lokaci na haifar da wata matsala.

“Ba kamar yadda sakon nan da ake ta yaɗawa ya nuna ba, barin takunkumi ba ya wani tasiri a iskar oxygen da mutum ke shaƙa bare har a kai ga batun shiga hadari,” a cewarsa.

“Barin takunkumin a fuska shi ne ya fi dacewa a duk inda mutum ya ke,” in ji Farfesa.

Amma ya ce idan mutum na cikin gidansa a zaune ba lallai ya sa takunkumin ba.

An fi so a sa idan za a shiga bainar jama’a ko a gida ko a waje

SHIN YAKAMATA IDAN MUTUM YANA TUKI A MOTARSA SHIKADAI YA SANYA TAKUNKUMI?

Farfesa ya ce babu laifi a wannan amma ba lallai ba ne.

“Ba a cika so mutum yana taɓa takunkumin ba saboda yana iya ɗaukar ƙwayoyin cuta da ke hannunsa ya sa a jikin takunkumin. Daga nan kuma su shiga jikinsa ta hanci ko ido ko baki.

“Don haka idan mutum ya riga ya sa takunkumin a fuskarsa kuma yana cikin motarsa zuwa wani waje yana iya barin takunkumin har ya isa inda zai je,” a cewar likitan.

Ya ce wannan na nufin an taƙaita yawan taɓawa saboda yawan sawa da cirewa ba shi da amfani.

“Gara a bar shi a fuskar da ya janye shi zuwa haɓa kamar yadda wasu ke yi,” in ji likitan.

Sai dai ya ce idan ba a riga an sa takunkumin ba aka shiga mota, mutum na iya bari sai ya isa inda zai shiga cikin mutane sai ya tsaftace hannunsa sannan ya sa takunkumin.

Short presentational grey line
Wace hanya ce mafi dacewa da za a sa takunkumin fuska?

Farfesa Isa ya ce da farko dai ya kamata a san cewa amfanin sa takunkumi shi ne don mutum ya kare kansa sannan ya kare mutanen da yake mu’amala da su daga cututtuka.

Ya bayyana cewa takunkumi na tare ƙwayoyin cuta daga shiga hanci ko baki.

“Da farko idan mutum zai sa wannan takunkumi kamata ya yi ya fara wanke hannu sa ruwa da sabulu sosai kafin ma ya taɓa takunkumi.

“Sannan ya kama igiyoyin biyu da ke jikin takunkumin a sa ta bayan kunnensa.

“Yana da kyau mutum ya san cewa lallai ne ya rufe hancinsa da habarsa, wannan ne zai tabbatar da takunkumin zai yi aiki yadda ya dace,” a cewar Farfesa Isa.

Ya kuma ce idan irin takunkumin nan ne mai launin shuɗi da fari wanda ake siya a kemis, mutum ya tabbata ya matse shi a karan hancinsa yadda babu wata babbar kafa a gefen karan hancin.

Kuma ɓangaren shuɗin shi ne zai fuskanci waje yayin da ɓanagren farin za a sa a fuska.

Farfesa Abubakar ya ce a guji sa takunkumi idan akwai danshi a fuskar mutum.

“Idan an yi alwala ko kuma idan an yi zufa, a tabbatar an tsane fuska kafin a sa takunkumi saboda idan akwai ƙwayoyin cuta a maƙale a fuska suna iya bin lemar nan su gangaro su shiga kafar hanci ko baki,” in ji likitan .

Don haka a tsane fuska tsaf sannan a sa takunkumin.

Haka kuma, Farfesa Abubakar ya ce ba a ko ina ake cire takunkumi a ajiye ba.

“A tabbatar da cewa wuri ne mai tsafta da aka goge da ruwa da sabulu ko sinadarin tsaftace wuri,” a cewarsa.

Ya ce shi ya sa ma hanya mafi dacewa ita ce kada a cire har sai an gama amfani da shi. Idan kuma ya zama dole a cire, abu mafi dacewa shi ne kada a maimaita takunkumin.

“A sa wani sabo wancan a yar da shi a shara musamman kwandon shara mai murfi,” in ji shi.

Amma ya ce idan takunkumi ne da aka ɗinka a gida, wato na yadi, ana so a wanke shi kullum da sabulu. Kuma idan da hali a sa dutsen guga a goge shi.

Farfesa Abubakar Isa ya ce wannan ne zai kashe duk wasu ƙwayoyin cuta da suka maƙale a jikin takunkumin.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *