
An kama jami’an tsaro bakwai masu ‘taimaka wa ƴan fashi’ a Zamfara
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama wasu jami’an tsaro bakwai a jihar bisa zarginsu da taimaka wa ‘yan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar. Gwamnatin ta sanar […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Duka da kokarin da ake a fadin duniya na ganin an kawar da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS a duniya, a Najeriya akwai mutum sama da miliyan 1.9 da ke rayuwa da cutar.
Hukumomi sun bayyana cewa kimanin mata masu juna biyu 124, 817 ne ke rayuwa da wannan mummunar cuta a jihar Ondo kadai.
Wannan na zuwa ne lokacin da za a bude wani shirin tallafa wa masu mafa da cuatar a Akure babban birnin jihar ta Ondo.
Sakataren gwamnatin jihar Oladunni Odu, wanda ya wakilci gwamna a yayin taron, ya ce adadin wadannan mutanen an same su ne kawai a cikin kananan hukumomi 18 na jihar.
Wadanda suka shirya taron sun yi alkawarin za su yi duk mai yiwuwa domin ganin an kawar da wannan cuta daga jihar.
Sun ce wannan cuta yanzu ba barazana ba ce kamar yadda ake ganinta a baya.
Bello Sani April 16, 2021
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama wasu jami’an tsaro bakwai a jihar bisa zarginsu da taimaka wa ‘yan fashi da makami a sassa daban-daban na jihar. Gwamnatin ta sanar […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)