
Yan bindiga sun kashe masunci a sabon harin da suka kai a Kaduna
Yan bindiga sun kashe wani masunci, Adamu Bala, a yayin da ya tafi rafi kama kifi a tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Alkali Hadiza Shagari ta babbar kotun tarayya dake Katsina ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi hukunci
Babbar kotun tarayya da ta samu shugabancin Mai shari’a Hadiza Shagari a ranar Laraba, ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi, Ibrahim Ali, hukuncin shekaru 15 a gidan yari babu tara.
Kafin a kama shi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Ali ya kasance mai safara tare da siyar da miyagun kwayoyi a garin Katsina.
A wata tattaunawa da manema labarai da hukumar NDLEA reshen jihar Katsina tayi, kwamandan hukumar, Momoudu Sule, ya sanar da manema labari cewa matashin mai safarar miyagun kwayoyin ya shiga hannu kuma an dinga mishi nasiha kada ya koma ruwa amma a banza.
A yayin da Sule yake kwatanta shekaru 15 a matsayin dogon lokaci, ya ce hakan zai dauke matashin daga titi kuma zai dakile yaduwar miyagun kwayoyi a garin Katsina tare da zama izina ga sauran masu irin halinsa.
“Mun tattara tare da mika shi gaban kotu a watan Nuwamba kuma da izinin Allah an yanke mishi hukunci.
“Ga Allah muke godiya, Ibrahim Ali a halin yanzu zai kwashe shekaru 15 a gidan yari ba tare da biyan tara ba.
“Shekaru 15 sun isa a dauke shi daga titi kuma miyagun kwayooyi zasu ragu a Katsina kuma hakan za ta kasance izina ga wadanda ke da hali irin nashi.
An yankewa Ibrahim Ali hukunci kuma an kaishi inda ya dace, wato gidan gyaran hali. A don haka nake kira ga wadanda ke irin wannan sana’a da su kara tunani saboda nan jihar Katsina ba wurinsu bane.
“Za mu zo kanku kuma zamu kama ku kuma zamu gurfanar da ku tare da tabbatar da cewakun karba hukuncin da ya dace,” Sule yace.
Yan bindiga sun kashe wani masunci, Adamu Bala, a yayin da ya tafi rafi kama kifi a tsakanin Zango da Ungwan Ruhogo a karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna, […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)