
Muna yajin aiki ne domin ganin karatun ƴaƴan talakwa ya inganta
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta yi watsi da Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya, wato IPPIS, a matsayin sharaɗin da […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Shugaban hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar wato KAROTA, Dakta Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa hukumar ta sa za ta tarawa jihar Kano haraji na naira biliyan Ɗaya da miliyan 500 a cikin shekara mai kamawa ta 2021.
Dakta Bappa Babba Ɗan-Agundi ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kuɗin hukumar a zauren Majalisar Dokokin Jihar Kano a yau Litinin.
Shugaban KAROTAR ya ƙara da cewa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya baiwa hukumar damar ɗaukar sabbin ma’aikata har 1,400.
Ya ce a halin da ake ciki, hukumar KAROTA ta ɗauki ma’aikata 700, zuwa Janairu, 2021 kuma za su ƙara ɗaukar wasu sabbin ma’aikatan 700.
A ƙarshe shugaban na KAROTA ya ce hukumarsa za ta haɗa kai da Hukumar Gyara Tituna ta Jihar Kano, KARMA, domin ganin sun tsaftace jihar.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta yi watsi da Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya, wato IPPIS, a matsayin sharaɗin da […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)