Ganduje ya yi magana kan shari’ar Sheikh Abduljabbar

Gwamnan Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta bibiyi batun Sheikh Abduljabbar Kabara “har zuwa karshensa.”

Mai magana da yawun Ganduje, Abba Anwar, ya ambato shi yana bayyana hakan ranar Juma’a yayin wata ziyara da ya kai wa Sheikh Qariballah Kabara, wanda yaya ne ga malamin.

Yana magana ne mako guda bayan an kai malamin gidan yari sakamakon gurfanar da shi a gaban wata kotun shari’ar Musulinci da ke jihar.

An gurfanar da malamin a gaban kotun ne a ranar Juma’a, bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.

Gwamna Ganduje ya kara da cewa “muna matukar farin ciki ganin cewa muna bin matakan da suka dace game da wannan batu. Kuma gwamnatin jiha za ta ci gaba da bibiyar lamarin sosai har zuwa karshensa.”

Gwamnan na Kano ya yaba wa malamin jihar ta Kano da suka tafka muqabala da Sheikh Abduljabbar game da zarginsa da yin batanci ga manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), yana mai cewa “fafutukar tamu ce duka.”.

Leave a Comment

%d bloggers like this: