play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Jihar Kano ta ware kudade N83.5m don yiwa dabbobi rigakafin

Siyasa

Jihar Kano ta ware kudade N83.5m don yiwa dabbobi rigakafin

Bello Sani February 17, 2021 10


Background
share close

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, ta bada kwangilar yiwa dabbobi rigakafi

A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da kwangilar Naira miliyan 83.4 don rigakafin dabbobi, The Nation ta ruwaito.

Yarjejeniyar ta hada da samar da kwalabe 8,250 na maganin rigakafin Bovine Pleuropneumonia (CBPP) da kuma kwalabe 20,000 na maganin rigakafin Peste des Petits Ruminants (PPR).

Shirin allurar rigakafin a duk fadin jihar, wanda zai fara nan da wasu makonni zai dauki shanu 800,000 da kuma kananan dabbobi miliyan 1 a kowace shekara.

Shirin allurar rigakafin za a aiwatar da shi ne ta hanyar shirin Bunkasa Aikin Noma da Makiyaya (KSADP), Kwararren Masanin Sadarwa Ameen K. Yassar, wanda ya bayyana a wata sanarwa a ranar Talata.

Ya bayyana cewa allurar rigakafin zata taka muhimmiyar rawa wajen inganta karfin dabbobi don yaki da cututtuka da kuma kula da jin daɗi da samar da manya da ƙananan dabbobi.

Ya bayyana cewa ba a gudanar da rigakafin dabbobi a jihar Kano ba a cikin shekaru uku da suka gabata kuma a sakamakon haka, yawancin al’ummomin makiyaya a jihar na fama da asarar dabbobi sosai.

Kodinetan ayyukan na jihar, Malam Ibrahim Garba Muhammed, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin hukumarsa, ya bayyana cewa an yi hakan ne don hana dubban iyalai makiyaya a daya daga cikin jihohin da suka fi yawan jama’a a Najeriya rasa ayyukansu.

A wani labarin, Sarkin Fulanin Abeokuta, Muhammad Kabir Labar a ranar Talata ya ce an kashe makiyaya 23 tare da kona gidaje kimanin 20 a rikicin kwanan nan a Jihar Ogun, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi magana a taron masu ruwa da tsaki kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana’antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al’adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami’ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Rate it
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *