Shugaban jam’iyyar APC Tinubu ya yabawa jihar Kano duba da zaman lafiya dake cikinta
Shugaban jam’iyyar Bola Tinubu, ya yaba da jihar Kano cewa ita ce jihar da tafi kowacce jiha zaman lafiya a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.
Tinubu ya fadi haka ne a taron bikin maulidinsa na karo na 12 da aka gudanar a jihar Kano don tunawa da ranar haihuwarsa da cikarsa shekaru 69 a duniya.
Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje game da nasarorin da ya samu musamman a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa.
Ya ce, “Jihar da ta fi zaman lafiya ita ce Kano. Da zarar kun samar da zaman lafiya, sada zumunci da kuma damar saka jari zai zo.”
Sai dai, Amurka da sauran kasashen yamma, sun shawarci ‘yan kasarsu da su guji zuwa Kano da wasu jihohi 13 saboda matsalar rashin tsaro.
Post comments (0)