play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Jama’ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

Labarai

Jama’ar gari sun cinna wa wani dan fashi da makami wuta a Yola

Bello Sani February 8, 2021

Background
share close

Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys’ a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, DSP, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Yola.

– Wasu fusatattun jama’ar gari sun afkawa wani da ake zargi da aikata fashi da makami a Yola

– Mutanen sun samu nasarar cinna wa dan fashin wuta kuma ya kone kurmus har lahira

– Rundunar ‘yan sandan Adamawa ta tabbatar da farruwar haka, kuma sun dauki gawar wanda aka kashen

Rundunar ‘yan sanda a Adamawa, a ranar Lahadi, ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da zama mamba a wata kungiyar gungun masu laifi da aka fi sani da‘ Shila Boys’ a Jimeta, karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasu ‘yan zanga-zanga sun kona dan kungiyar Shila har lahira bisa zargin cewa ya yi wa wata mata sata da kuma daba mata wuka, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar, DSP, Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Yola.

Nguroje ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 7:00 na dare.

Ya ce an dauki gawar wanda ake zargin ne daga rundunar Jimeta da ke Jimeta.

Ya fadawa NAN cewa mambobin kungiyar su uku, suna kan keke ne yayin da suka yi wa matar fashin a hanyar Mubi da ke Jimeta.

“Matar (an sakaya sunanta) ta yi ihu don neman taimako kuma nan take, wasu fusatattun mutane suka bi wadanda ake zargin, suka kama daya daga cikinsu suka cinna masa wuta.

“Sauran ‘yan kungiyar biyu kuwa, sun tsere,’’ Nguroje ya fada wa NAN.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *