play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Insha Allahu ba za’a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari

Siyasa

Insha Allahu ba za’a taba wani yakin Basasa a Najeriya ba, Shugaba Buhari

Bello Sani March 27, 2021 7


Background
share close

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi waiwaye kan yakin basasan da aka kwashe watanni 30 ana yi a Najeriya kuma ya yi addu’a kada Allah ya maimaitawa Najeriya irin wannan yaki.

Mai magana da yawun shugaban kasan, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya sake mai taken “Shugaba Buhari ya aika ta’ziyya ga shahidan yakin basasan Najeriya.”

Najeriya, karkashin Janar Yakubu Gowon ta shiga yaki da Biyafara da suka balle karkashin jagorancin Laftanar Kanar Odumegwu Ojukwu tsakanin 6 ga Yulin 1967 da 15 ga Junairun 1970.

Shehu ya ce Buhari ya yi waiwayen ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban mazhabar Tijjaniyya, Sheikh Muhammadul Mahy Niass.

“Buhari ya ce a watanni 30 da akayi yakin basasa, an yi rashin rayukan yan Najeriya kuma ya yi addu’an kada mu sake ganin irin wannan yaki.”

A cewar Garba Shehu, Buhari ya yi maraba ga Khalifan kuma ya jinjinawa kokarin da sukeyi wajen kawo karshen matsalar tsaron da kasar ke fuskanta.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: