play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Indonesia na yunƙurin samar da dokar haramta shan Barasa a faɗin ƙasar

Labarai

Indonesia na yunƙurin samar da dokar haramta shan Barasa a faɗin ƙasar

Bello Sani November 25, 2020 6


Background
share close

Ƴan majalisar dokokin ƙasar Indonesia sun kara ta da batun kudurin dokar da zai ta haramta amfani da barasa a faɗin kasar.

Hakan na faruwa ne yayin da ake samun yawaitar mace-mace sanadiyyar shan barasar da aka hada ba tare da an bi ka’ida ba.

Sai dai masu sukar wannan kuduri sun ce, haramta shan barasar baki daya, zai kara ta’azzara amfani da barasa mai hadari da aka hada ba bisa ka’ida ba.

Majalisar wakilan kasar dai ta saka wannan batu cikin muhimman batutuwan da za ta fi mayar da hankali akansu a shekara mai zuwa, karkashin tsarin da ke fayyace muhimman batutuwan da suka shafi kasa.

A shekarar 2015 aka fara gabatar da kudurin amma aka jingine shi yayin da ya fuskantar suka.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *