
An Halarta shan Giya da Karuwanci a ƙasar Dubai
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wasu sauye-sauye a dokokin shari’ar Musuluncin ƙasar inda ta halasta shan giya da yin zina. Sauyin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Mataimakiyar Sakare Janar na Majlisar Dinkin Duniya, Amina J Mohammed,ta kalubalanci matan ƙasar nan kan su kara jajircewa wajen ganin sun karbi ragamar shugabancin Najeriya idan shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.
Amina wacce ke jagorantar manyan jami’an majalisar da ke wata ziyarar aiki a Najeriya ta bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja.
Tun da farko dai sai da tawagar ta gana da shugaba Buhari a fadar sa ta Aso Rock inda suka tattauna a kan hanyoyin sake gina kasar bayan mummunar illar da annobar COVID-19 ta yi mata.
Amina, wacce tsohuwar Ministar Muhalli ce a Najeriya ta ce dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye wajen gina kasa ba tare da la’akari da banbance-banbancensu na siyasa ba.
Ta ce, “Ya kamata mu fahimci abinda yake daidai domin muga ya faru, a rukuninmu ko a daidaikunmu. Akwai bukatar girmama kowanne bangare na kasarmu saboda kowa na da irin gudunmawar da zai bayar wajen gina kasa.”
Da aka tambayeta ko tana da sha’awar tsayawa shugabancin idan Buharin ya kammala mulki sai ta ce, “Wannan sh ine fata na, bana tunanin mace ba za ta iya ba. Na yi amannar cewa duk wanda ya yi kokari zai iya cimma burinsa.
“Saboda haka dole mata su tashi tsaye. Suna da kusan kaso 50 cikin 100 na kuri’un da ake kadawa, idan har za su iya neman goyon bayan maza, me zai hana su cimma burinsu? Ban ga dalilin da zai sa ace mace ba za ta mulki Najeriya ba.
A cikin watan Disambar shekarar 2016 ne Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nada Amina Mohammed a matsayin mataimakiyarsa.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi wasu sauye-sauye a dokokin shari’ar Musuluncin ƙasar inda ta halasta shan giya da yin zina. Sauyin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)