
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Hukumar da ke rajistar katin ɗan ƙasa a Najeriya, NIMC, ta fara kira ga ƴan ƙasar da su sauke manhajar ta NIMC a wayoyinsu, bayan hukumar ta ƙaddamar da ita domin ƴan ƙasar su iya yin tozali da katinsu a wayoyinsu ba wai lallai sai a zahiri ba.
NIMC ta bayyana cewa manhajar da ta fito da ita ba ta da wuyar amfani, haka kuma duk wanda zai yi amfani da ita lallai sai yana da lambar NIN.
Kamar yadda hukumar ta NIMC ta bayyana, hukumar sadarwa ta Najeriya wato NCC ta bayyana cewa mutum zai iya haɗa lambarsa ta NIN da lambobin layi bakwai – waɗanda aka yi musu rajista da sunansa.
Ta yaya mutum zai sauke manhajar NIMC a wayar?
A farko dai, za ku iya sauke manhajar daga Google Play Store idan kuna amfani da waya ƙirar Android, haka kuma ga masu amfani da iPhone za su iya zuwa Apple Store domin duba manhajar domin su sauke.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)