
Yanzu-yanzu: Dalibai 7 cikin 317 da aka sace sun samu kubuta daga hannun yan bindiga
Wata majiya ta bayyana cewa daliban sun dawo gida da kansu bayan sun samu ikon sullubewa yan bindigan a cikin daji. Sun kara da cewa tun daga cikin dajin suka […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Bello Sani February 27, 2021 11
Gwamnatin jihar Kano ta bada umurnin rufe makarantun kwana guda 10 a sassan jihar
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantun kwana 10 a sassan jihar nan take biyo bayan sace yan matan makarantar GGSS Jangebe a jihar Zamfara, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Muhammad Kiru ya ce gwamnatin ta cimma matsayin ne bayan nazari da bita kan abubuwan da ke faruwa a jihohin da ke makawabtaka da ita inda ake sace dalibai.
cewarsa, rashin tsaron ne ya tilastawa gwamnatin daukar matakin domin kare lafiya yaran.
Ya ce iyaye da masu kulawa da yara su tafi su kwashe yaransu daga makarantun, nan gaba gwamnati za ta sanar da ranar da za a bude makarantun don cigaba da karatu.
Ya lissafa makarantun da abin ya shafa kamar haka: Maitama Sule Science College, Gaya; Boarding Secondary School, Ajingi; Girls Secondary Schools a Sumaila, Gezawa da Jogana, Kachako da wani a Unguwar Gyartai a Kunchi da kuma Girls Secondary School, Albasu,
Sauran sun hada da Makarantar Sakandare ta maza da ke Maiyaki da Unity College a Karaye.
Wata majiya ta bayyana cewa daliban sun dawo gida da kansu bayan sun samu ikon sullubewa yan bindigan a cikin daji. Sun kara da cewa tun daga cikin dajin suka […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)