
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Rahotanni daga sassa daban-daban na ƙasar nan na bayyana yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi; inda masu karamin karfi musamman ke ji a jika.
Haka kuma Talauci a ƙasar nan sai karuwa yake yi. Mutane na tsananin jin jiki. Abinci tsada, kayan masarufi tsada, tsadar rayuwa, komai tsada. Wadannan su ne labaran da ake ji daga mafi yawan jihohin ƙasar nan.
Hakazalika kuma al’ummar ƙasar nan su na matukar kokawa da yanayi na matsin rayuwa da ake fama da shi, musamman na karancin kudaden biyan bukatu na yau da kullum a hannun jama’a.
Wannan dai yana zuwa ne tun bayan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rufe iyakokin ƙasar nan a cikin watan Agustan shekarar 2019 da zummar daƙile yawaitar fasa-kwauri da kuma bunƙasa tattalin arziki, ko da yake ‘yan kasar nan da dama sun koka kan matakin.
Masana da masu sharhi akan al’amauran yau da kullum su ke bayyana ra’ayinsu akan wannan matsalar da ake fama da ita. Nasiru Salisu Zango ɗan jarida ne a birnin Kano ya bayyana cewa talakawan Najeriya su na fama da tsananin wahalar rayuwa Nasiru Zango ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk.
“Shinkafa ƴar gida Naira dubu 23, ta waje naira dubu 27, Masara da Gero, sun doshi naira 500 kwano ɗaya”
Ya ƙara da cewa a ɓangaren kudin wutar lantarki nan ma talaka bai tsira ba, haka ma ma’aikatan gwamnati ba su da tabbacin samun cikakken albashi.
“Ana shirin ƙara kudin lantarki, kwanakin baya an ƙara farashin fetur, ma’aikaci ba shi da tabbacin albashin sa domin kullum ana yi masa funce, Dan kasuwa ya fita an kore shi daga in da ya ke kasuwancin sa, direba ya fito aiki kuskure kadan an ci tarar sa dubu 10, gashi babu tabbacin inda tarar ke zuwa”
“Marasa lafiya na kwance a gida suna jiran naira dubu 2 ko fiye domin sayen magani, an bude gidan kallo, an bar makarantu a rufe, malaman islamiyya, ba kudin wata balle na Laraba, malaman makarantu masu zaman kansu suna jiran tsammani su da iyalansa”
Haka shi ma wani malamin jami’a, Mubarak Ibrahim Lawan ya bayyana ra’ayinsa game da irin halin da talakwan Najeriya su ka samu kan su a ciki.
“Litar mai ta zama N161, buhun shinkafa yana tskanin 19 da 25k, Dollar ta kai N450 zuwa 470, jinin manoma, makiyaya, ‘yan sanda da na sojoji yana ta zuba kullum a ƙauyuka”
“Noma da kiwo suna neman gagara. Ga satar rashin kunya ta jam’ian gwamnati ta na ƙara balagewa. Sun raina talaka irin yadda suka raina shugaban ƙasar tunda “toothless, clawless (and clueless) cat” ne, wato Magen Lami, ba cizo ba yakushi!
“Wallahi, ko a mulkin Abacha da aka yi yunwa da fatara bai kai wannan lokacin taɓarɓarewa ba. Tunda a can akwai zaman lafiyar da ya fi na yanzu. Kuma talakan da ke cikin talauci shi ke jin jiki, ba a qyanqyashe sabbin talakawa”
“Amma yanzu, da gaske fa rarraba talauci gida-gida ake yi, don haka ƙyanƙyasar gawurtattun fuƙara’u ake yi, kuma ga rashin zaman lafiya na ta hauhawa”
Ana kallon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na rufe iyakokin ƙasa nan a matsayin abin da ya shafi kasuwancinsu, ya kuma janyo hau-hauwar farashin kayyiyaki da dama.
A farkon wannan watan na Satumba kamfanonin samar da hasken wutar lantarki a fadin kasar nan suka fara amfani da sabon farashin wutar lantarki.
Kamfanonin sun dauki matakin ne bayan sauyin da hukumar sanya ido kan harkokin wutar lantarki ta kasar nan wato NERC ta yi.
Ana kukan targaɗe kuma sai ga karaya ta samu, domin al’ummar ƙasar nan ba su gama jimamin ƙarin matsin rayuwar da su ka tsinci kan su ba, sai kwatsam su ka ji sanarwa daga hukumar Kayyade Farashin Man Fetur da Dangoginsa ta ƙasa PPPRA, ta kara farashin man fetur a kasar nan, inda a yanzu za a rinka sayarwa da ƴan kasuwa Naira 151 da kwabo 51 su kuma su sayar da shi akan naira 161 akan kowacce lita.
Abin tambayar shi ne yaushe talakawan Najeriya samu sauƙin rayuwa?
Labarai24.com
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)