Gwamnatin tarayyar najeriya ta bude abon portal mai suna NEXIT domin yan N-Power batch A da B. Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a 27 ga watan nuwamba 2020 inda ta kara da cewa anyi wannan tsarin ne da hadin gwiwan babban bankin kasar najeriya watau Central Bank.
Wannan tsarin zai taimaka wa yan N-Power da suka gama karbar kudaden alawus dinsu don samin shiga tsare-tsaren dogaro da kai na babban bankin kasa
Sabon portal din NEXIT zai bi wasu hanyoyi da babban bankin kasa ta tsara domin tantance wadanda suka cancanta su shiga tsare-tsaren dogaro da kai.
Post comments (0)