Gwamnatin Najeriya ta ce ma’aikatar lafiya na yunƙurin fara amfani da allurar Depot Medroxyprogesterone Acetate Subcutaneous domin ƙarfafa tsarin iyali a ƙasar, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.

Ƙaramin Ministan Lafiya Olorunimbe Mamora ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin gwamnatin tarayya na tsarin iyali ga kafafen yaɗa labarai, wanda aka yi ta intanet ranar Alhamis.

“Wannan wata hanya ce ta haɓaka samar da kayayyakin tsarin iyali domin bai wa ‘yan Najeriya damar yin zaɓi da kansu,” in ji shi.

“Maganin wanda ake bai wa mutane damar yi wa kansu allura da kansu, ana kallonsa a matsayin wanda zai kawo gagarumin sauyi a harkokin tsarin iyali a Najeriya.

“Yana amfani matuƙa wajen tabbatar da ɗorewar amfani da magani musamman a ƙauyuka ta hanyar bai wa mutum kwalaben maganin bayan an ba shi horo kan yadda za a yi amfani da shi.”

  1. Har yanzu tsarin iyali bai karɓu ba a wasu sassa na Najeriya yayin da aka yi ƙiyasin yawan al’ummar ƙasar zai kai miliyan 260 nan da 2030

Leave a Comment

%d bloggers like this: