
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗi kan wani riga-kafin korona na jabu dake yawo a faɗin ƙasar.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna NAFDAC ta ce ba ta amince da ko wane riga-kafi ba.
Shugabar hukumar Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa ta tashi tsaye haiƙan wajen hana shigar riga-kafin na jabu hannun jama’a ba.
A baya-bayannan hukumomi sun ce suna fatan yi wa kaso 40 cikin ɗari na ƴan kasar riga-kafin a 2021.
Yayin da ake fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da cutar ta korona, akwai fargabar cewa wasu miyagu ko ƙungiyoyi za su iya amfani da halin da ake ciki su samar da riga-kafin da ba a amince da shi ba a kasuwannin bayan fage.
A ranar Alhamis cutar ta kashe mutum 23 a Najeriya, wanda shi ne mafi yawa tun bayan da korona ta ɓulla a Najeriya, kuma adadin waɗanda suka kamu ya kai 105,478 a cikin wata goma sha ɗaya.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)