play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Gwamnatin Kaduna ta ceto wasu daga hannun ‘yan bindiga

Tsaro

Gwamnatin Kaduna ta ceto wasu daga hannun ‘yan bindiga

Bello Sani March 13, 2021 30


Background
share close

Tun farko, wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojoji sun yi nasarar kuɓutar da ɗalibai da yawa kafin ‘yan bindigar su gudu da su.

“Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130.

Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba”, in ji Aruwan.

Kawo yanzu kusan ɗalibai 800 aka sace tun watan Disamba kuma wannan ne karo na uku da aka sace ɗalibai daga makarantunsu a shekarar 2021 a Najeriya.

A jihar Kaduna kaɗai, ‘yan bindiga sun kashe mutum 937 sannan suka yi garkuwa da 1,972 a shekarar 2020.

Sanarwar ta kuma cewa dakarun soji ne suka kai dauki cikin makarantar, inda suka fafata da ‘yan bindigar.

Wasu daga cikin daliban da aka ceto sun samu raunuka, kuma ana duba lafiyarsu a wani asibitiin sojoji na Kaduna, a cewar sanarwar.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *