Shugabar kwalejin koyar da jinya tare da ungwan zoma, Rukaiya Shettima Mustapha ta samu takardar tuhuma a kan dakatar da wasu dalibai da tayi kan cewa basu bi ayari sun fita tarar shugaba Buhari ba.

Juliana Bitrus, wacce ita ce kwamishinan lafiya ta jihar ta aike da wasikar tuhumar inda take bukatar karin bayani kan lamarin cikin sa’o’i 48.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuni.

A wasikar mai kwanan wata 25 ga Yuni, Juliana ta nisanta gwamnatin jihar daga matakin da Mustapha ta dauka inda tace ta yi aikin ne ta gaban kanta.

Kwamishinan ta kwatanta lamarin da ya faru da mara dadi, inda ta kara da cewa wannan hukuncin tayi shi ne babu tuntubar kowa balle ma’aikatar lafiya.

Ta ce shiga ayari a tari shugaban kasa abu ne da dalibai suka saba amma babu wanda ya taba matsa musu yin hakan.

Kwamishinan ta nuna jimaminta inda tace shugabar kwalejin tayi amfani da zuwan shugaban kasar ne inda ta kai ga wasu dalibai da take hari.

Leave a Comment

%d bloggers like this: