Gwamna Nyesom Wike ya na zargin sojojin saman Najeriya da karkatar da wasu jirage da su ka samu ta hannun gwamnatin Ribas.
Mai girma Nyesom Wike ya ce kudin wadannan jiragen yaki masu saukar ungulu sun haura Dala miliyan 10, kusan Naira biliyan hudu.
Gwamnan ya ce a maimakon sojojin su yi amfani da wadannan jirage wajen maganin masu satar danyen mai, sai aka tafi da su Arewa.
Nyesom Wike ya bayyana cewa yanzu haka ana aiki da wadannan jirage a yankin Arewa maso gabas wajen yakar ‘yan ta’addan Boko Haram.
Gwamnan ya yi barazanar karbe jiragen ruwan da ya ba sojojin kasa, da sojojin ruwa, da ‘yan sanda, muddin su ka kai su wasu jihohin.
Gwamna Wike ya bayyana haka ne yayin da ya ke gabatar da wadannan kayan aiki ga jami’an tsaro a gidan gwamnatin Ribas a Fatakwal.
Jaridar The Nation ta rahoto dakarun sojojin saman kasar ta na cewa ba za ta biye wa gwamnan na Ribas ba, ta ce zargin abinda yake yi siyasa ce.
Commodore Edward Gabkwet, ya karyata wannan zargi.
A cewar gwamnan, “Gwamnatin Ribas ta batar da sama da $10m wajen sayen jiragen yaki masu saukar ungulu, da za a yaki masu satar mai a nan.”
Amma ku tambaye ni ina wadannan jirage su ke yau? Hedikwatar sojojin sama ta karbe su, sun ce ana amfani da su wajen yakar ‘Yan Boko Haram.”
Post comments (0)