
Masu Garkuwa Da Mutane Hanyar Abuja zuwa Kaduna Sun Dawo Aiki
A ranar Alhamis ne masu garkuwa da mutane suka dawo kan babbar hanyar Abduja zuwa Kaduna, inda ake zargin suna ci gaba da garkuwa da matafiya da ba a san […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya caccaki sojoji bisa harin da aka kaiwa tawagar sa a garin Baga na Karamar hukumar Kukuwa.
Gwamna Zulum dai ya bar Birnin Maiduguri ne a yammacin ranar Litinin zuwa arewacin jihar domin cigaba da rabon kayan abinci wanda ya fara tun farkon watan Yuli.
A ranar Laraba ya tsara zuwa garin Baga garin dake kusa da tafkin Chadi wanda ya taya da kayar baya suke rike da shi a shekarun baya har sai da jami’an tsaro suka kwace garin.
Sai dai tazarar kila mita kadan da garin yan bindiga suka bude wuta kan tawagar Gwamnan. Sai dai jami’an tsaron dake tsare da lafiyar gwamnan sun mayar da martani ga maharan.
Zulum wanda yake cikin fushi ya caccaki jami’in sojan dake kula da yankin Mile 4 bisa gazawar sojojin wajen hana yan ta’adda mamayr garin Baga.
“Kun kasance anan tsawon shekara guda , akwai sojoji 1,181 anan, idan baza ku iya kare garin Baga ba wanda yake kasa da kilomita biyar daga sansanin ku toh ya kamata mu manta da Baga. Zan fadawa babban hafsan soja na kasa ya kawo mazaje a sauran gurare da zasu yi amfani. Inji Zulum.
A ranar Alhamis ne masu garkuwa da mutane suka dawo kan babbar hanyar Abduja zuwa Kaduna, inda ake zargin suna ci gaba da garkuwa da matafiya da ba a san […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)