play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kiwon Lafiya
  • keyboard_arrow_right Fiye da mutum miliyan 60 ne ba sa samun isashshen bacci a Najeriya

Labarai

Fiye da mutum miliyan 60 ne ba sa samun isashshen bacci a Najeriya

Bello Sani November 28, 2020 7


Background
share close

Bincike ya nuna akalla mutum miliyan sittin da uku a Najeriya ne basa samun isashshen barci a kowacce rana.

Likitoci sun ce da dalilan da kan jawo rashin wadataccen bacci sun hada da rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa da matsalolin kasuwanci, da rashin tsaro, da hidimomin iyali da kuma rashin kwanciyar hankali a wuraren aiki ko cikin al’umma.

Wasu mutanen ba sa bacci kuma ba su fara kafa hira sai a lokacin da dare ya yi, kuma sukan kwashe tsawon lokaci suna hirar akan al’amurra daban-daban har safiyar Allah.

Bincike ya nuna akwai dalilai ma su yawa da ke hana mutum samun isasshen bacci, watakila a sabili da damuwa ko kuma zumudin wani abu ko kuma rashin samun koshin lafiya.

Duk da cewa wasu mutanen sun san da cewa akwai illar da ke tattare da rashin samun cikakken bacci amma suna ci gaba da yin hira mai tsawo da dare.

To ko me likitoci ke cewa?

Bacci kamar yadda likitoci suka nuna wani abinci ne da dan adam kan bai wa jikinsa kuma wata hanya ce ta gina lafiyar kwakwalwa da samun koshin lafiya.

Dakta Hassan kwararren likita ne a jihar Kano, ya gargadi masu kwashe tsawon dare ba sa bacci da su dinga takaita hira mai tsawo musanman a lokacin da jiki ke bukatar hutu.

Dakta Hassan ya ce ” Samun bacci alamu ne na samun koshin lafiya ga bil’adama. Duk mutumin da ba ya samun isasshen bacci – to zai iya kamuwa da hawan jini. Wadda a sakamakon haka zai iya kamuwa da wasu cututtuka.”

Ya kara da cewa ”Ana kiran rashin samun wadataccen bacci insomania- kuma in ciwon insomania ya yi yawa yakan haifar wa mutum aikata wasu abubuwa kamar na mai tabin hankali. Wannan ne ya sa ake bukatar mutum ya samu bacci a tsawon sa’o’i shida zuwa takwas.”

Bincike ya nuna wasu daga mutane na shan kwayoyi da za su hana su yin bacci a tsawon dare.

A kasashe kamar Japan da Saudi Arebiya da Philliphine da Sweden da kuma Indiya mutane ba sa wuce tsawon sa’o’i shida suna bacci.

To amma a kasashe kamar Birtaniya da Finland da New Zealand akalla suna samun tsawon bacci kamar na sa’o’i bakwai da rabi a kowanne dare.

A Afirka babu wani takamaiman tsari ko tsawon sa’o’i a mtasayin alkalumman da za a dogara da su na bacci tsakanin kasashe.

Sai dai an tabbatar da cewa matsalolin rayuwa da ke tattare da al’ummar nahiyar za su zama kadan daga dalilan rashin samun wadataccen bacci.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *