
Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi a ƙasar nan wato NDLEA, ta ce kusan kashi 14 da rabi na al’ummar kasar nan na shan tabar wiwi ko hodar ibilis ko kuma kodin da ke tagayyara hankalinsu.
Daraktar da ke Yaki da Masu Amfani da Haramtattun Kwayoyi a Hukumar NDLEA Titus-Awogbuyi Joyce ta sanar da haka sakamakon alkaluman da hukumar ta tattara a shekarar 2018.
Jami’ar ta ce, alkaluman sun kuma bayyana cewar, daga cikin mutane 4 da ke ta’ammuli da wadannan miyagun kwayoyi guda mace ce, abin da ke nuna yadda matsalar ta shafi kowanne bangare.
Hukumar Yaki da Amfani da Miyagun Kwayoyin ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 246 suka yi amfani da irin wadannan kwayoyi a duniya daga shekarar 2014.
Hukumar ta NDLEA dai ta dade tana neman da a tsaurara hukunci a kan masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.
Post comments (0)