play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Sarauta
  • keyboard_arrow_right El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru

Labarai

El-Rufai ya nada Usman a matsayin sabon Sarkin Kauru

Bello Sani April 12, 2021 26


Background
share close

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya nada Alhaji Ya’u Shehu Usman, tsohon Sarkin Fadan Kauru, a matsayin sabon Sarkin Kauru

Usman, Shugaban Hukumar Kula da Kasafin Kudi ta Jihar Kaduna, an haife shi ne a ranar 15 ga Mayu, 1955 a Kauru kuma ya fara aiki da Ma’aikatan Jihar Kaduna a 1977.

Sabon basaraken ya yi ritaya a 2012 a matsayin Darakta, Ma’aikatar Kudi (MoFI), Ofishin Akanta Janar na Jihar Kaduna.

Akanta, Usman ya kasance tsohon Shugaban karamar Hukumar Giwa, Sakataren karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, kuma mai kula da Majalisar Karamar Hukumar Zangon Kataf.

Ya kuma kaance memba na Kwamitin mika mulki ta Jihar Kaduna kuma memba a hukumar bunkasa birane ta jihar Kaduna (KASUPDA).

A gefe guda, Sarkin masarautar Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya tsige Ciroman Zazzau Alhaji Sai’du Mai Lafiya daga kujerarsa.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sarkin ya tube rawanin Ciroman Zazzau ne saboda zargin rashin biyayya da girmama masarautar.

Ciroman Zazzau mai shekaru 84 a duniya ya kasance daga cikin manyan‘Yan Majalisar Sarki kuma Dan uwan Sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ne na kut-da-kut.

A wani labarin kuma, Mai martaba Sarkin Lere, Birgediya Janar Abubakar Garba Mohammed (mai murabus) ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 77 a duniya.

Wata majiya daga garin na Lere da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa Legit.ng Hausa rasuwar sarkin.

Garba ya rasu ne a safiyar ranar Asabar 10 ga watan Afrilu a Kaduna bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *