play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Dole ‘yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Siyasa

Dole ‘yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara

Bello Sani March 26, 2021 9


Background
share close

Darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan ‘yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.

Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.

Kamar yadda yace, wannan al’amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.

Ya zama dole ga kowannen mai hali ko kungiya da su fitar da wani kaso na dukiyarsu a matsayin Zakka,” yace.

Abubakar ya kara da yin bayanin cewa hukumar ta zo da wannan sabon salon ne ta yadda kowanne mai hannu da shuni zai biya zakka,

“‘Yan majalisun jihar, ballantana na kwamitin lamurran addinin sun zauna tare da tattaunawa a kan muhimmancin Zakka.

“A matsayinmu na kwamitin, muna kokarin kaiwa matsaya ta yadda duk mai neman wata kujera a jihar sai ya bada shaidar yana biyan Zakka ga hukumar,” yace.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *