Tsohon tsageran yankin Neja-Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya kalubalanci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya na furta gwamnatin Biyafara.
Daily Trust ta rahoto cewa Mujahid Asari Dokubo ya fito ya bayyana kansa a matsayin shugaban wata kungiya ta Biafra defacto Customary Government.
Asari Dokubo ya sanar da haka ne a wani jawabi da wani Uche Mefor ya fitar a matsayinsa na shugaban sashen yada labarai da sadarwa na tafiyar BCG.
Uche Mefor ya ce:
“Mu a matsayinmu na mutanen Biyafara, mun tsaida cewa lokaci ya yi da za mu dauki matsayarmu a hannunmu, mu da kanmu da ‘ya ‘yanmu da sauran al’ummomin da za ayi a nan gaba, ‘yanci.”
“Na ‘dan dakata kadan, amma na gode wa Ubangiji, lokaci ya yi da za mu yi aikinmu, mu bauta wa kasarmu, na karbi wannan nauyi, zan sadaukar da rayuwa ta 100% a kai.”
Aikina na farko shi ne in bayyana wadanda za su zama ‘yan gaba-gaba a wannnan tafiyar inji Asari Dakubo.
A jawabin ne aka nada George Onyibe da Emeka Emeka Esiri a matsayin sakatare da mai bada shawara kan harkar shari’a na Biafra defacto Customary Government.
Post comments (0)