play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Tsaro
  • keyboard_arrow_right Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja

Labarai

Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja

Bello Sani April 8, 2021 8


Background
share close

Wani kudiri da ke gaban majalisar wakilan tarayya ya na neman halattawa mata amfani da hijabi a wajen aikin gidan soja da sauran aikin khaki.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Honarabul Saidu Abdullahi mai wakiltar Bida/Gbako/Katcha a majalisar wakilan tarayya ne ya gabatar da kudirin.

Wannan kudiri ya samu karbuwa, har ya kai mataki na biyu a zauren majalisar wakilan kasar.

Saidu Abdullahi wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin tattalin arziki ya yi wa kudirin take da: ‘Religious Discrimination (Prohibition, Prevention)’

Sashe na 13 na kudirin zai bada damar duk macen da ta ke bukata, ta rika amfani da hijabi, ba tare da an tsangwame ta a gidan soja ko wurin aiki ba.

“Duk wanda aka dauka aikin jami’in tsaro a gidan soja ko makamancinsu, ba zai gamu da tsangwama saboda zabin koyarwar addininsa ba.”

Rahoton ya ce kudirin zai halatta amfani da tambarin addini, kallabi (‘dan-kwali) da kuma hijabi.

Idan kudirin ya samu karbuwa, za a hukunta duk wanda aka samu da laifin tsangwamar masu sanya hijabi, amma kudirin bai tsaida hukuncin laifin ba.

Kudirin da ke neman samun shiga ya ba manyan kotu damar hukunta masu tsangwama, sannan hukumar NHRC za ta rika sauraron korafin jami’an tsaro.

Kwanakin baya kun ji sai da Ma’aikatar ilimi ta jihar Kwara ta sake garkame makarantu 10 da ta ba damar budewa saboda rikicin da ake yi game da sa hijabi.

Gwamnatin jihar Kwara tace ta yi hakan ne saboda lamarin tsaro sakamakon rikicin da ake yi saboda kotu da gwamnati sun bada damar sa hijabi a makarantu.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *