
Haɗaɗɗiyar ƙungiyar shugabannin ɗaliban jami’o’in jihohi a arewacin Nijeriya, wato Coalition of 19 Northern States Students Union Government Presidents ta ce ta bai wa gwamnati wa’adin kwana shida ta daidaita da ƙungiyar malaman jami’o’i wato ASUU.
Ƙungiyar ɗaliban ta ce ta cimma wannan matsaya ne bayan wani taro da ta yi a Kano, inda ta ce muddin gwamnatin Najeriya da ASUU suka gaza cimma matsaya nan da mako guda to za su shiga zanga-zanga.
Bugu da kari kungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta gano ɗaliban da aka sace a jihar Kaduna da kuma magance matsalolin fyaɗe da suka yi katutu a sassan ƙasar.
Kwared Abdulrahman Zanna Sunoma shine jagoran ƙungiyar, ya kuma tabbatar wa da BBC cewa za su fara zanga zangar matsawar bangaroran biyu su ka kasa cimma matsaya nan da mako guda.
A cewar Kwamred Zanna ‘mun hango cewa dalibai idan suna zaune a gida ba sa komai shi ya sa suke shiga wadansu ayyuka da kasa ba ta so.’
‘Mun tattauna a kan cewa mun ba da kwana shida ma kungiyar ASUU da gwamnatin Tarayya su zauna su zo matsayi daya a bude makarantu a koma, in ba haka ba mu kungiyar dalibai na arewaci za mu fito gaba daya daliban arewcin Najeriya mu fada wa gwamnati abinda ya ke damunmu’.
Kwamred Zanna ya kara da cewa ‘mun zauna mun jira tsawon wata takwas mun ba wa shugabanni dama da lokaci su tafi su sasanta lamarinnan amma abu ya ki ci ya ki cinyewa’.
To sai dai ya ce suna fatan bangaroran biyu za su nemo mafita kawo karshen yajin aikin kafin wa’adin na kwanaki shida da su ka basu ya cika.
Ko a farkon makonnan sai da daliban jami’o’in su ka bayyana damuwa game da kiran da ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta yi wa mambobinta cewa su nemi wata hanyar dogaro da kai.
Bugu da kari kuma ASUU ta sanar da iyaye da su kansu ɗaliban jami’o’in da kada su sa ran komawarsu makaranta a nan kusa.
Kuma Matakin biyo bayan zargin da ƙungiyar malaman jami’o’in ta yi wa gwamnati, na nuna halin ko-in-kula wajen biyan buƙatunsu, da kuma dakatar da biyansu albashi tsawon wata takwas.
BBC Hausa
Post comments (0)