play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Addini
  • keyboard_arrow_right Da dumi duminsa: An ga wata a Najeriya, gobe za’a tashi da azumi: Kwamitin duban wata

Labarai

Da dumi duminsa: An ga wata a Najeriya, gobe za’a tashi da azumi: Kwamitin duban wata

Bello Sani April 12, 2021 16


Background
share close

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa an ga jinjirin watan Ramadana a wurare daban-daban a Najeriya, mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar.

Hakazalika Kwamitin neman wata a Najeriya ce tayi wannan sanarwa a shafinta na Tuwita.

A jawabin da yayi kai tsaye, Sarkin Musulmi ya ce an ga watan Ramadana na shekarar 1442 AH.

Ya yi kira ga Musulmai su fara azuni kuma su koma ga Allah lokacin wannan wata mai alfarma.

Ya bukacesu su roki Allah ya kawo karshen matsalar tsaro da annobar Korona a Najeriya.

Sultan ya yi addu’an cewa Allah ya baiwa Musulami daman gabatar da ibadunsu kuma ya yi kira ga Musulman su bi dokokin da aka gindaya na kariya daga annobar Korona.

A jawabin da majalisar koli ta sharia’ar Musulunci a Najeriya NSCIA ta saki, tace: “NSCIA karkashin jagorancin shugabanta kuma Sultan na Sokoto na sanar da daukacin al’ummar Musulmi cewa an ga jinjirin watan Ramadana a yau 12/04/2021 wanda yayi daidai da 29 Sha’aban. 1442AH.

Rate it
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *