
A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke kukan rashin cancantar ciwo wani bashin dala milyan 1.2 da Najeriya za ta yi daga ƙasar Brazil, gwamnatin Najeriya ta sake neman amincewar Majalisar Dattawa ta ciwo wani sabon bashi na dala milyan 750.
Sai dai wadannan kudaden daga Bankin Duniya za a ciwo su, kuma a madadin jihohi za a ciwo basussukan domin bunkasa tattalin arziki a garuruwa da karkara, kuma a inganta tare da tallafa wa wadanda ba su galihu har su rika samun wadataccen abinci.
Ministar Harkokin Kudade Zainab Usman, ta ce shirin na daya daga cikin hanyoyin tayar da komadar dukan da tattalin arziki ya yi wa jama’a sanadiyyar barkewar korona.
Ta yi wannan bayani a wurin kaddamar da Kwamitin Farfado da Tattalin Arziki Bayan Korona.
Zainab Ahmed, ta tabbatar da cewa tulin bashin da ke kan Najeriya zai kai naira tiriliyan 38.68 nan da watan Disamba, 2021.
Minista Zainab ta yi wannan kintacen ne ranar Talatar makon jiya a gaban Kwamitin Bin Biddigin Basussukan Cikin Gida da Waje da ake bin Najeriya, a zauren Majalisar Dattawa.
Post comments (0)