play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Buhari ka ji tsoron Allah ka cika alkawarin da ka yiwa talakwa – ACF

Siyasa

Buhari ka ji tsoron Allah ka cika alkawarin da ka yiwa talakwa – ACF

Bello Sani November 25, 2020 7


Background
share close

Kungiyar Dattawan Arewacin Ƙasar nan ta ACF ta ce, matsalar tsaro ta tsananta a yankin arewacin Najeriya, tana mai kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ji tsoron Allah, sannan ya cika alkawuran da ya yi wa ‘yan kasar nan na samar da zaman lafiya.

Kungiyar ta bayyana cewa, shugaba Buhari ya fi kowa sanin laifin da ke tattare da rantsuwa da al-Kur’ani mai girma ba tare da cikawa ba.

Ƙungiyar ACF ta ce, ta damu matuka kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kashe al’umma a yankin arewacin Najeriya duk da ikirarin Ministan Kula da Ayyukan ‘Yan sanda da ke cewa, an ci galabar ‘yan bindigar.

A cikin sanarwar da ta fitar, ACF ta ce, tana wakiltar dimbin al’ummar arewacin Najeriya wajen isar da fushinsu ga shugaba Buhari da zummar ganin ya gaggauta daukar mataki.

ACF ta yi tur da sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma sace daliban Jami’ar Ahmadu Bello su tara.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *