play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona

Siyasa

Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona

Bello Sani March 7, 2021 3


Background
share close

Fadar shugaban kasa ta shaidawa ‘yan Najeriya cewa rigakafin Korona na da tasiri mai kyau.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai sha wata wahala ba bayan yin allurar AstraZeneca ta Korona, TheCable ta ruwaito.

Buhari da Osinbajo sun yi allurar rigakafin a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Asabar.

A wani yunkuri na kawar da fargabar ‘yan Najeriya, Shehu ya tabbatarwa ‘yan kasar amincin allurar rigakafin, yana mai cewa shugaban “ya ji garau ya ci gaba da harkokinsa” bayan an yi masa rigakafin.

Ya kara da cewa idan har akwai illoli, to fadar shugaban kasa ba zata yi rufa-rufa akai ba.

“A cikin amsa ga tambayoyin manema labarai, ina so in tabbatar wa dukkan ‘yan kasa, kuma in kawar da tsoro da rashin fahimta game da lafiyar allurar rigakafin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, SAN a safiyar yau,” in ji Shehu a cikin sanarwa.

“Bayan ya sami jab din sa, Shugaban kasan ya sami nutsuwa ya kuma ci gaba da aikin sa. Idan akwai wasu illoli da suka biyo baya, za mu kasance a buɗe game da hakan amma har yanzu babu wani abu na illa, mai tsanani ko taushi ga Shugaban. Yana ci gaba kamar yadda ya saba.

“Muna fatan wannan zai taimaka wajen isar da sako mai karfi a tsakanin mutane, musamman wadanda ke kokawa game da inganci da amincin allurar.”

Bayan yin allurar, Buhari ya bayyana shawarar da ya yanke na yin allurar a bainar jama’a a matsayin “nuna jagoranci da imani kan aminci da ingancin alluran”.

Shugaban ya ba da shawarar allurar ga duk wani dan Najeriya da ya cancanta, yana mai cewa tana da matukar kariya daga kwayar cutar.

“Na yi allurata ta farko kuma ina so in ja hankalin duk ‘yan Najeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga kwayar, cutar” in ji shi.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *