play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Ilimi
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta

Ilimi

Budurwa ta kalubalanci mutane da su shiga gasar rubutu mai kyau, ta wallafa hoton littafinta

Bello Sani February 17, 2021 102


Background
share close

Wata ‘yar Najeriya, Maryam Shehu, ta haddasa cece-kuce mai ban sha’awa game da yin rubutu da fasahar rubutun hannu a makarantu

Wata matashiya yar Najeriya, Maryam Shehu, ta baiwa mutane da yawa mamaki da kyakkyawan rubutunta yayin da ta nemi wanda yake ganin ya isa su zo suyi gasa.

A wani sako da ta wallafa a ranar Litinin, 15 ga watan Fabrairu, budurwar ta sanya ɗaya daga cikin litattafanta na makaranta don nuna baiwar da Allah ya yi mata na iya rubutu.
Wasu mabiya shafin Twitter da suke ganin suma gwanaye ne a wajen rubutu suma sun wallafa nasu.

Lokacin da mutane suka ce lamarin zai sha bamban idan ana karanto mata tana rubutawa, sai budurwar ta nuna musu ba haka ba inda ta sake wallafa hoton wani rubutun nata.

matasaradio.com ta daukko wasu daga cikin sharshin mabiyanta :

@unilorinamebor ya ce: “Baba wai a inda kuke samun irin wannan kyawawan rubutu a koda yaushe. Ni nawa kamar tsuntsu na caccakar ƙasa.”

@lukmanadeola2 ya ce: “Zan so in ga rubutunki a lokacin da malamin makarantar sakandaren da ke jin yunwa ke karanto maki jawabai kina rubutawa.”

@Nigerianbreed20 ya ce: “Na tabbata ba rubutun ana fada kina rubutawa bane! saboda rubutunki ba zai kyan wannan ba yayin da malami ke fada kina rubutawa…. Ko yaya dai yayi kyau!”

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *