play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Duniya
  • keyboard_arrow_right Biden zai soke dokar hana wasu ƙasashen musulmai shiga Amurka da Trump ya sanya

Labarai

Biden zai soke dokar hana wasu ƙasashen musulmai shiga Amurka da Trump ya sanya

Bello Sani January 17, 2021 9


Background
share close

Yayin da ake dakon rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka a ranar Laraba, tawagar zaɓaɓɓen shugaban ta bayyana jerin dokokin da Trump ya sanya da yake shirin sokewa a ranar da aka rantsar da shi.

Shugaban ma’aikata na Mista Biden Ron Klain ya ce da zarar an rantsar da Biden, zai mayar da Amurka cikin yarjejeniyar sauyin yanayi, sannan ya soke haramcin shiga kasar daga wasu kasashen musulmai da shugaba Trump ya sanya.

Yanzu haka dai yawan dakarun da aka jibge a birnin Washington domin tabbatar da an yi bikin rantsuwar lafiya ya ninninka yawan dakarun kasar a kasashen Afghanistan da Iraqi.

Dukkanin jihohin Amurka 50 da Gundumar Columbia na cikin shirin ko ta kwana saboda yiwuwar samun zanga-zanga a karshen makon nan, gabanin bikin rantsar da sabon shugaban kasar Joe Biden a ranar Laraba.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *