play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Siyasa
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno

Siyasa

Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno

Bello Sani March 14, 2021 7


Background
share close

Hukumar EFCC tace bata da tabbacin za ta binciki tsoffin shugabannin tsaron da suka gabata

Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta magantu a kan fallasar da Manjo Janar Babagana Monguno yayi na cewa makuden kudade na siyan makamai sun bace.

Monguno ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da BBC Hausa a ranar Juma’a da ta gabata.

Amma bayan caccakar da ya sha, ya janye kalamansa inda ya zargi kafafen yada labarai da rashin fahimtar inda ya dosa.

Tattaunawarsa da BBC Hausa ta bayyana cewa babu rashin fahimta a cikin abinda jama’a ke yadawa, illa iyaka abinda ya sanar kenan.

A kan ko hukumar ta fara binciken lamarin, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren yace ba zai iya bada tabbacin cewa hukumar za ta binciki tsoffin hafsoshin tsaron ba.

Ya ce babu wata shaida da ta bayyana gaban hukumar wacce ke nuna cewa tsoffin hafsoshin tsaron sun kwashe kudin makamai kamar yadda mai bada shawara kan tsaron kasa yayi ikirari.

“Ba mu da wata shaida ko zargi. Muna aiki ne da abinda muka gani ba wai abinda za a ce zai iya yuwuwa ba,” Uwujaren ya sanar da Daily Trust.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *