Wata Kungiyar agaji dake ceto bakin da suka makale a cikin teku tace yanzu haka wasu bakin haure 270 na cikin mawuyacin hali a tekun meditereniya inda suke bukatar kai musu dauki, yayin da jiragen ‘yan kasuwa suka ki taimaka musu.
Kungiyar tace bakin 270 na fuskantar hadari sosai ganin yadda akayi watsi da su akan teku na sa’oi da dama ba tare da kai musu agaji ba, inda suke fuskantar nitsewa a ciki.
Sanarwar kungiyar tace jiragen ruwan dake dauke da bakin guda 2 na dauke da mutane 110 kowanne daga cikin su, yayin da na 3 ke dauke da mutane 60.
Kungiyar ta zargi jami’an tsaron gabar ruwan Malta da Italia da kin kai musu dauki.
Post comments (0)