Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.
Gwamnan ya ce kudin wata-wata da ake rabawa gwamnoni bai kai ba, sai da gwamnatin tarayya ta buga sabbin kudi bilyan 50 zuwa 60 aka raba musu.
“Lokacin da aka biyamu kudin wata-wata na Maris, sai da gwamnatin tarayya ta buga N50-N60 billion don kudin su isa a raba mana,” Obaseki ya bayyana ranar Alhamis.
“A wannan watan na Afrilu, zamu sake komawa Abuja a raba mana kudi. A karshen shekarar nan adadin bashin da muka ci zai zama tsakanin N15-N16 trillion.”
Kawai karban bashin kudi akeyi babu hanyar biya, amma hankalin kowa na kan 2023, kowa na ganin laifin shugaban kasa sai kace boka ne.”
“Najeriya ta canza. Tattalin arzikin Najeriya ya canza gaba daya tun bayan yakin basasa, kawai kame-kame mukeyi.”
Post comments (0)