
WHO ta gargaɗi Musulmin Duniya kan ƙaratowar Watan Azumin Ramadhan
Kwanaki kaɗan kafin zuwan watan Ramadan da kuma na ista, ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulman duniya kan dokokin kare yaɗuwar korona. WHO ta ce ya kamata ƙasashen […]
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Da alama har yaanzin ministan Sadarwa Isa Pantami na kan bakarsa na rufe layukan waya waɗanda ba’a haɗa su da NIN ba
Wata ƙungiyar masu amfani da kamfanonin sadarwa tace bata amince da ƙarin wa’adin da gwamnatin tarayya ta yi ba kan haɗa layukan waya da lambar katin zama ɗan ƙasa (NIN).
Ƙungiyar tace yakamata gwamnati ta bi umarnin da kotu ta bayar na ƙara lokacin har tsawon wata biyu.
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa, ƙungiyar ta ce ƙarin wata ɗaya ya yi kaɗan kuma tana kira ga gwamnatin tarayya ta yi biyayya ga hukuncin da kotu ta yi ran 23 ga watan Maris.
A kwanakin baya dai wata babbar kotu dake zamanta a Lagos ta bada umarnin ƙara wa’adin rijistar NIN da tsawon wata biyu.
Mai shari’a M.A. Onyetenu ya bada umarnin ya yin da yake yanke hukunci kan ƙarar da lauyan dake fafutukar kare hakkin ɗan adam, Monday Ubani, ya shigar.
Lauyan ya shigar da ƙarar ne yana neman kotun da ta dakatar da ma’aikatar sadarwar kasar nan daga shirin ta na rufe layukan waya waɗanda ba’a haɗa su da NIN ba.
Sai dai shugaban ƙungiyar masu amfani da kamfanonin sadarwa na ƙasar nan ya kira yi ma’aikatar sadarwar ƙasar nan da ta yi biyayya ga hukuncin kotu.
A cewar shugaban: “Bamu yarda da karin wata ɗaya ba, ya kamata ma’aikatar ta yi biyayya ga abinda kotu tace, ta ƙara wata biyu.”
Darakatan yaɗa labarai na hukumar kula da sadarwar ƙasar nan (NCC), Dr Ikechukwu Adinde, ya bayyana matsayar gwamnati na ƙara wa’adin wata ɗaya.
Ya ce an amince da ƙarin ne a wani taro da aka gudanar ran Alhamis tare da masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa wanda ministan sadarwa Isa Pantami ya jagoranta.
Ya kuma ƙara da cewa shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da wannan ƙarin na wata ɗaya.
Kwanaki kaɗan kafin zuwan watan Ramadan da kuma na ista, ƙungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta gargaɗi musulman duniya kan dokokin kare yaɗuwar korona. WHO ta ce ya kamata ƙasashen […]
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)