play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Ba gaskiya bane mutuwar tshohon kwaminshinan ‘yan sandan jahar kano

Labarai

Ba gaskiya bane mutuwar tshohon kwaminshinan ‘yan sandan jahar kano

Bello Sani February 10, 2021 7


Background
share close

Tsohon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ke Najeriya CP Muhammad Wakili, ya ƙaryata wasu rahotanni da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa yayin wani hatsarin mota

Da daren ranar Talata ne wasu labarai da ke bayyana rasuwarsa sakamakon hatsarin mota suka bazu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka riƙa sanya hotunansa, suna fatan Allah ya ji ƙansa.

Sai dai yayin zantawa da BBC, CP Muhammad Wakili mai ritaya, ya ce yana nan da ransa, cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

“Ban san ta ina wannan labari ya fito ba, ban san mene ne dalilinsu ba, ban san me suke son su cimma da wannan abu ba, wannan al’amari ya sa mutane damuwa, tun 11 na dare ake ta kira na domin a tabbatar da gaskiyar wannan labari,” in ji tsohon kwamishinan ‘yan sandan wanda aka fi sani da Singham.

Ya ƙara da cewa ya samu labarin ne sakamakon kiransa da wani babban mutum ya yi, bayan kiciɓis da irin waɗancan labarai da ya yi a shafukan sada zumunta, abin da ya sa hankalinsa ya tashi ya kira wayarsa domin ya tabbatar ko gaskiya ne.

‘Ina da lambarsa, na faɗa a raina, lafiya kuwa da daren nan na ga kiransa?, na ɗagawa na ce yallaɓai lafiya?, sai kawai na ji yana ta cewa Alhamdulillahi… Alhamdulillahi.. ai ga abin da ke faruwa ana ta cewa ka rasu,” in ji Muhammad Wakili.

Ya kuma yi kira ga masoyansa, su kwantar da hankalinsu, yana cewa yana nan cikin ƙoshin lafiya.

Shi dai tsohon kwamishinan CP Wakili ya samu dumɓin masoya a Najeriya, sakamakon ficen da ya yi wajen yaki da masu sha da hada-hadar miyagun ƙwayoyi a jihar Kano lokacin da yake matsayin kwamishinan ƴan sanda a jihar.

Ya yi ritaya ne a shekarar 2019, inda yanzu yake riƙe da muƙamin mai bai wa gwamnan jihar Gombe shawara a kan harkokin tsaro.

 

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *