
Gaba Tsakanin Makota Bello Sani
Hatsarin mota ya cika da ayarin motocin Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno.
Mutane biyu sun mutu sakamakon hatsarin da ya cika da ayarin motocin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.
Jaridar TheCable ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri.
Zulum na dawowa ne daga karamar hukumar Mafa (LGA) inda ya je sabonta rijistarsa na dann jam’iyyar All Progressives Congress (APC) lokacin da hatsarin ya faru
Wata majiyar ‘yan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce wani basarake na daga cikin wadanda suka mutu
A cewar ‘yan sandan, motar da ke dauke da Mai-Kanuribe, wani hakimin Borno da ke Legas, ta kife bayan da tayar ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kuma wani fasinja guda daya.
An garzaya da mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti yayin da aka kai gawarwakin mutanen biyu da suka mutu zuwa Maiduguri.
Copyright Matasa Radio - by Bello Sani
Post comments (0)