play_arrow

keyboard_arrow_right

skip_previous play_arrow skip_next
00:00 00:00
playlist_play chevron_left
volume_up
chevron_left
  • Home
  • keyboard_arrow_right Labarai
  • keyboard_arrow_right Kimiyya da Fasaha
  • keyboard_arrow_right Arewa ga naku: Ƴar Kano ta ƙera manhajar shigar da ƙorafin fyaɗe

Labarai

Arewa ga naku: Ƴar Kano ta ƙera manhajar shigar da ƙorafin fyaɗe

Bello Sani March 9, 2021 6


Background
share close

Matashiya haifafar jihar Kano ta ƙera manhajar android na kai rahoton fyaɗe.

Wata matashiya haifafar jihar Kano, Saadat Aliyu ta ƙera manhajar android mai suna ‘Helpio App’ domin kai rahoto kan fyaɗe, Channels Television ta ruwaito.

An kaɗamar da ‘Helpio App’ a playstore a ranar 6 ga watan Agustan 2020.

Saadat Aliyu wacce ta kafa Shamrock Innovations, cibiyar Fasaha ta Mata da Matasa a Kano ta ce kowa na iya zuwa Playstore ya sauke manhajar a wayarsa.

“Za ka iya zuwa Playstore, ka nemo shi sannan ka sauke sai ka yi rajista da imel ɗin ka cikin harshen Hausa ko Ingilishi,” kamar yadda ta shaidawa Channels Television a ranar Litinin.

“Kawo yanzu kuna wayarka. Daga nangiyar tallafawa wadanda aka ci zarafinsu, marayu da marasa galihu (ISSOL) da wata ƙungiyar na tallafawa gajiyayu, kare hakkin yara da walwalarsu (EDCRAW) sun yi rajista a manhajar.”

Ta ce ta fara koyon fasahar sadarwa ne daga wurin ɗan uwanta a lokacin tana ajin ƙaramar sakandare daga bisani ta koya da kanta har ta zama mai ƙera manhaja

Matashiyar ta ce nan ba da dadewa ba za ta ƙaddamar da wata sabuwar manhajar ta mai alaka da fasaha da kuɗi da ake fatan zai taimakawa mata da sauran jama’a.

Rate it
Previous post
Post comments (0)

Leave a reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *