Ma’aikatar wasanni ta ce ba za a sake rabawa Matasa tallafin ruwan kudi ba
Gwamnatin tarayya ta daina bada ruwan kudi a matsayin tallafi ga matasa, ta ce za ta koma ba matasan aron kudi ne a Najeriya.
Jaridar Punch ta rahoto Ministan matasa da cigaban wasanni na kasa, Sunday Dare ya na wannan bayani a garin Awka, jihar Anambra.
Ministan ya yi jawabi ne a karshen taron kwanaki biyu na kara wa juna sani da hukumar aikin gona ta IITA, Ibadan ta shirya a Awka.
IITA ta gudanar da taron ne tare da cibiyar binciken aikin gona ta Umudike da cibiyar International Fund for Agricultural Development.
A cewar Ministan, ba a raba kason tallafin da ake ware wa domin matasa, a wasu wuraren ma ya yi ikirarin ana facaka ne da kudin.
“Ganin haka, mu ka yanke ba za a sake bada tallafi ga matasa ba, a maimakon haka za a rika ba su bashi ne da za su biya bayan wani lokacin da aka yarje, ta yarda wasu dabam za su amfana da irin wannan tsari.” inji Ministan kasar.
Dare ya ce gwamnati ta kirkiro kafafe dabam-dabam da matasa za su amfana ta harkar gona ta hanyar kafa cibiyoyi a Kudu da Arewa.
Mataimakin darektan bangaren koya wa matasa sana’a da abin yi a ma’aikatar wasanni da matasa, Adamu Usman Kaina, ya wakilci Minista.
Adamu Usman Kaina ya ce matasa 4600 sun amfana da tallafin N500, 000 da gwamnatin tarayyata bada domin rage radadin annobar COVID-19.
Post comments (0)