
Bayan samun rahotan sace shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa da mahara suka yi da daren ranar Asabar a lafiya, an tsinci gawarsa a yau Lahadi.
Tun da farko mahara sun afkawa gidan shugaban jam’iyyar APC na jihar Nasarawa Philip Shekwo, a cikin daren ranar Asabar a gidan sa dake Lafiya suka yi awon gaba da shi.
Wani jigo a jam’iyyar APC na jihar, ya tabbatarwa da jaridar PREMIUM TIMES aukuwar hakan da kuma tsintar gwarasa da ka yi.
A jiya ne dai ƴan bindigar su ka yi garkuwa da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Philip Tataru Shekwo.